NCC ta Umarci Kamfanonin Sadarwa da su Buɗe Layukan Wayoyin da aka Rufe

 

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya ta umarci kamfanonin sadarwa da su gaggauta buɗe layukan wayoyin da aka rufe saboda rashin haɗa layukan da lambar ɗan ƙasa ta NIN.

Darakta yaɗa labarai na hukumar, Reuben Muoka ne ya bayyana haka ranar Litinin.

Cikin wata sanarwa da NCC ta fitar, Muoka ya ce abokanan hulɗar kamfanonin ba sa iya amfani da layukan nasu saboda sun gaza haɗa lambobinsu na NIN da layukan wayoyinsu.

Sanarwar ta ce a ƙarshen makon nan ne, masu amfani da layukan sadarwa suka fuskanci ƙalubale wajen amfani da layukan wayoyinsu saboda rashin haɗa lambobinsu na NIN da layukansu.

“Hakan ya sa an toshe layuka da dama bisa dokoki da ƙa’idojin jaɗa NIN da layukan waya.” in ji sanarwar.

Tun Disambar 2023, hukumar ta NCC ta ke nazari kan wa’adin da aka ɗiba na haɗa NIN da layukan waya, an saka 15 ga watan Afrilu a matsayin wa’adin rufe layukan da ba a haɗa su da lambar NIN ba.

An kuma sake tsawaita wa’adin zuwa 31 ga Yulin 2024 domin bai wa kwastamomi dama su miƙa lambobinsu na NIN domin a tantance.

Sai dai duk da tswaita wa’adin, wasu layukan ba a haɗa su da NIN ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here