NCDC ta Tabbatar da Bullowar Sabuwar Cuta a Jahohi 7 a Fadin Najariya

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a jahohi bakwai a fadin kasar.

Jahohin da sabuwar cutar ta billo sun hada da Kano, Plateau, Bauchi, Gombe, Nasarawa, Niger da kuma Kaduna.

Ihekweazu ya ce tuni NCDC ta gwada wasu samfuran dan Adam kan cutar A daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da magance cutar COVID-19, cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a jahohi bakwai a fadin kasar.

Avian Influenza wani nau’in kwayar cutar mura ce wacce ta fi shafar tsuntsaye, amma kuma tana iya harbar mutane.

Jaridar The Cable, ta ambaci NAN, ta ruwaito cewa Chikwe Ihekweazu, babban darakta na NCDC, yayi magana kan barkewar cutar a ranar Talata, 6 ga Afrilu, yayin da yake bayar da bayanai game da yanayin annobar cutar da ayyukan maganceta a Najeriya.

A cewar shugaban NCDC din, ya zuwa ranar 24 ga Maris, jihohi bakwai sun ba da rahoton bullar cutar ta Pathogenic Avian Influenza (HPAI) (H5N1) a cikin tsuntsaye. Ya lissafa jihohin da abin ya shafa kamar haka:

1. Kano

2. Plateau

3. Bauchi

4. Gombe

5. Nasarawa

6. Niger

7. Kaduna

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Ihekweazu ya ce tuni NCDC ta gwada wasu samfuran dan Adam kan cutar.

Ya bayyana:

“An karbi jimlar samfuran mutane 83 kuma an gwada 64 (kashi 87.7 cikin 100). Daga cikin samfurin da aka gwada, bakwai (10.9 bisa dari) sun kasance dauke da murar A, shida 85.7 sun kasance da nau’ikan A / H5 yayin da kashi 14.3 cikin dari bai da rukuni.”

Ihekweazu ya ce daga cikin 83 da aka ruwaito, 27 sun fito ne daga kananan hukumomin Nasarawa, Ungogo da Gwale (LGA) a cikin jahar Kano.

Ya ce sun kasance 18 daga kananan hukumomi biyu (Jos ta arewa da kudu) a Filato; 19 daga kananan hukumomi biyu (Bauchi da Toro) a jahar Bauchi, da kuma 19 daga kananan hukumomi uku (Kaltungo, Yamaltu Deba da Gombe) a jahar Gombe.

Shugaban na NCDC ya bayyana cewa sakamakon gwajin ya nuna cewa jahohi biyu sun bayar da rahoton mutane bakwai da suka kamu da cutar-Kano hudu da Filato uku.

Ya ce duk wadanda suka kamun sun kasance manoma, ma’aikatan gona, masu kula da tsuntsaye, da kuma ‘yan kasuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here