Shugaban Hukumar NCDC ya yi Magana Kan Rigakwafin Korona

 

Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC), Dr. Chikwe Ihekweazu, a ranar Alhamis ya ce rigakafi ne hanya daya tilo na kawo karshen annobar Korona, The Nation ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa hanyoyin dakile yaduwar cutar irinsu wanke hannu, amfani da sinadarin tsaftace hannu, amfani da takunkumin rufe baki da baiwa juna tazara, kawai zasu iya rage yaduwar ne amma ba zasu iya kawo karshen annobar ba.

Ihekweazu ya kara da cewa hukumar NSCDC, kwamitin PTF da ma’aikatar lafiya zasu ilmantar da yan Najeriya kan muhimmancin rigakafi, wanda za’a samu watanni ukun farkon shekarar 2021.

Yace: “Babu wani magani a tarihin likitanci, babu ko guda, da ya kare rayuka a tarihin dan Adam kamar rigakafi.”

“Rigakafi kawai wasu abubuwan ban mamaki ne a fannin Likitanci. Mun kawo karshen cutar shan inna da bakon dauro gaba daya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here