Mataimakin Shugaban NLC ya yi Alla-wadai da Karin Kudin Wutar Lantarki

 

Hukumar NERC ta baiwa kamfanonin raba wuta umurnin kara farashin lantarki daga yau.

Mataimakin shugaban NLC ya yi Alla-wadai da wannan abu.

Wannan kari ya biyo bayan karin farashin iskar gas na girki a fadin tarayya.

Abuja – Mataimakin shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Joe Ajaero, ya yi kira ga gwamnatin tarayya kada ta sake ta kara farashin kudin wutan lantarki.

Ajaearo ya bayyana hakan yayin hira da yan jarida a shirin Kakaaki na tashar AIT ranar Talata.

Dan kwadagon wanda shina Sakatare Janar na kungiyar ma’aikatan wutan lantarki ya ce ta wani dalili NERC zata kara kudin wuta bayyan ba’a karawa ma’aikata kudin albashi ba.

Ya kara da cewa kamfanonin raba wuta (Discos) na kokarin daurawa talakawa nauyin gazawarsu.

Yace:

“Bara da wannan lamari ya taso, NLC ta sa baki kuma aka kafa kwamitin mutum bakwai karkashin jagorancin karamin ministan kwadago, Festus Keyamo.Ni mamban kwamitin ne.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here