Ƙungiyar NCYP ta Magantu Kan Yarjejeniyar da Gwamna Uba ya Cimmawa da Kamfanin China
Jihar Kaduna – Ƙungiyar matasan kiristocin Arewa (NCYP), ta ba gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani shawara.
Ƙungiyar NCYP ta buƙaci Gwamna Uba Sani ya guji tafka irin kura-kuran da magabacinsa Nasir El-Rufai ya yi a yayin da yake ƙulla yarjejeniya da ƙungiyoyin ƙasashen waje a madadin jihar.
An yabawa Gwamna Uba Sani
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NCYP, Isaac Abrak, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Cable.
Shugaban NCYP ya yabawa gwamnan bisa rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin Huawei na ƙasar China.
Read Also:
Isaac Abrak ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata gagarumar nasara da za ta iya inganta ɓangaren ICT na jihar da kuma samar da sababbin damammaki ga matasa.
“El-Rufai ya bar Kaduna da bashi”, NCYP
Ya yi tsokaci kan gwamnatin El-Rufai da ta karɓo lamunin $350m daga bankin duniya domin bunƙasa ilimi wanda daga ƙarshe ba a cimma manufar da ta sanya aka karɓo shi ba.
“Muna kira ga gwamnati da ta guji yin irin kura-kuran da aka yi a baya, musamman waɗanda aka yi a gwamnatin da ta shuɗe ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai da ta ci bashin $350m domin bunƙasa harkar ilmi.”
“Abin takaici ba a cimma manufar wannan bashin ba, sannan a yau an bar mutanen jihar Kaduna da nauyin biyan bashin da bai amfanar da komai ba.”