Ali Ndume ya Bawa Shugaba Buhari Shawara
Ali Ndume, sanatan Jihar Borno ta kudu, ya shawarci shugaba Buhari ya yi sauye-sauye a kunshin gwamnatinsa.
Sanata Ndume ya ce shugaba Buhari mutumin kirki ne da ke da kyakyawar niyya amma akwai masu mugun nufi a tattare da shi.
A cewar Sanata Ndume, shugaba Buhari ya kafa tarihi a bangaren aiwatar da kasafin kudin.
kasa Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu kuma shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattijai, Mohammed Ndume, ya buƙaci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi canje-canje a gwamnatinsa matuƙar yana nufin Najeriya da alheri a shekarar 2021.
Read Also:
Sanatan ya yi wannan furucin ne jiya Litinin yayin da yake ganawa da yan jaridu a gidansa da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Koda ya ke ya ce shugaba Buhari mutum ne nagari amma akwai waɗanda ke ƙoƙarin kawo cikas ga yunƙurinsa na inganta rayuwar yan Najeriya.
Sanata Mohammed Ndume ya ce “Ina matuƙar farin ciki da aiwatar da kasafin 2020 da kusan kaso 90, nasarar da ba’a taɓa samu ba a tarihin ƙasar nan.”
“Abin baƙin ciki kuma shine hakan bai taɓa wasu guraren da ya kamata ba musamman a yankin arewa maso gabas saboda rashin wakilci da mukamai marasa amfani.”
Da ya ke magantuwa kan nasarorin da ya cimma a yankin da ya ke wakilta, sanatan ya ce daga 2019 zuwa yanzu, karo na huɗu da aka zaɓe shi, yana cikin waɗanda suka fi kowa samun nasarar aiwatar da kudirorinsu a mazaɓunsu.