ALLAH ya yi wa Kanin Sarkin Daura Abdullahi Umar Rasuwa

Abdullahi Umar, kanin Sarkin Daura, Mai martaba Umar Faruk Umar ya riga mu gidan gaskiya.

Umar ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ta ritsa da shi da abokansa biyu a ranar Lahadi a hanyar Katsina/Daura.

Gwamnan Kstaina, Aminu Bello Masari ya tafi fadar sarki don yi masa ta’aziyyar rasuwar kaninsa da sauran mutanen biyu.

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, ya rasa kaninsa, Abdullahi Umar sanadiyyar hatsarin mota da ta ritsa da shi, The Punch ta ruwaito.

Umar ya rasu ne sakamakon mummunan hsatarin mota a hanyar Katsina/Daura a ranar Lahadi tare da abokansa biyu.

A halin yanzu ba gama samun cikaken bayani kan yadda hatsarin ya afku ba amma Gwamna Aminu Bello Masarri na jihar Katsina a ranar Litinin ya yi wa sarkin Daura ta’aziyyar rasuwar kaninsa.

Mai bada shawara na musamman kan ilimin makarantun gaba da sakandare, Dr Bashir Ruwangodiya da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka yi wa gwamnan rakiya zuwa ta’aziyyar.

Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, Atoney Janar na Jihar, Barrista Ahmed El-Marzuq da Ambasada Adamu Sai’du ne suka tarbi gwamnan da tawagarsa a fadar sarkin.

Gwamna Masari ya kuma ziyarci gidajen sauran mutanen biyu da suka rasu inda ya yi wa iyalansu jaje.

Ya yi addu’ar Alllah ya jikanssu ya kuma bawa iyalansu hakurin jure rashin.

Marigayi Abdullahi Umar ya rasu ya bar matar aure daya da yara takwas da yan uwa da dama ciki har da Sarkin Daura.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here