Ali Ndume ya yi Magana Kan Hare-Haren Boko Haram

 

Sanata Ali Ndume ya yi watsi da hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai jihohin Adamawa da Borno.

Yan ta’addan sun kai harin ne a daren ranar Kirsimeti.

Ndume ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa ransu a harin.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Sanata Ali Ndume, a ranar Juma’a, ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram a kauyen Pemi da ke jihar Borno da garin Garkida da ke karamar hukumar Gumbi jihar Adamawa a daren Kirsimeti.

Garin Garkida ya kasance daya daga cikin wuraren da mishan suka fara zama a arewacin Najeriya.

Makasan sun bad da kamanni a matsayin masu aikin leburanci, a cewar wani dan shekara 24 da ya tsira daga kisan gillar.

Ndume da yake martani a kan mummunan al’amarin, ya bukaci rundunar soji da ta zama a ankare maimakon mayar da martani bayan aikin gama ya gama.

Ya bukace su da su ci gaba da addu’a don dorewar zaman lafiya a kasar.

Ndume ya ce: “Wannan abun bakin ciki ne cewa yan ta’adda sun sake kai hari a ranar Kirsimeti sannan suka kashe mutum biyar a Pemi.

“An ce an lalata cocina, asibitoci da makarantu a yayin harin.

“Ina amfani da wannan damar wajen mika jaje ga iyalan mamatan yayinda ya kamata sojoji da ke yankin su dunga kasancewa a ankare da yan ta’addan maimakon yin martani bayan aikin gama y agama.”

Rahotanni daga yankin Garkida ya nuna cewa yan ta’addan sun kai mamaya garin ne ta babban hanyar da ke sada yankin da Biu a jihar Borno.

Mutanen yankin sun bayyana cewa an tursasa jama’a tserewa daga garin zuwa tsaunuka yayinda yan ta’addan suka sace kayayyakin abinci da kona gidaje a tsaka da harbi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here