Ndume: Rage Albashin ‘Yan Majalisu ba Zai ƙara Komai a Tattalin Arziƙin Kasa ba

Sanata Ali Ndume ya yi korafi a kan kira da mutane ke yi na a rage albashin yan majalisun tarayya

Ndume ya ce babu wani tasiri da zabtare albashin yan majalisun zai yi a tattalin arzikin kasar – Dan majalisar ya ce biliyan N128 kacal aka ware wa majalisun cikin kasafin kudin triliyan N13 na 2021 Sanata Ali Ndume ya soki kira da ake yi na rage albashin mambobin majalisar dokokin tarayya, ya ce a ganinsa albashin yan majalisar bai da kowani tasiri kan tattalin arziki. “Bai da kowani tasiri a kan tattalin arziki,” In ji Ndume a shirin Channels Television na yammacin ranar Juma’ a, lokacin da aka tambaye shi game da tasiri albashin yan majalisa kan tattalin arzikin kasar. Dan majalisar mai wakiltan Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin cewa mambobin majalisar dokokin na tarayya sun samu naira biliyan 128 ne kacal a kasafin naira tiriliyan 13 na 2021.

“A wajena, sukar majalisar dokokin tarayya, a soke NASS. Hakan na nufin za a samu ragin naira biliyan 128 amma shin akwai wani banbanci da hakan zai kawo? Saboda wannan abu (kira ga rage albashin mambobin majalisar tarayya) ya yiwa mutane irina da suka fito domin yin aiki, ba wai don azurta kansu ba yawa.”

Ndume ya yi korafin cewa babu wani dan majalisa da ya taba tara kudi saboda ya kasance a majalisar tarayya. “Babu wani dan majalisa, ku je ku duba tarihi, babu wanda ya zama mai kudi saboda ya taba rike mukamin dan majalisa,” in ji Ndume.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here