Jahar Neje ta Kara Kudin Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai Sama da N200,000
Bayan na Kaduna, jami’ar jahar Neja ta kara kudin makaranta.
Dalibai sun nuna bacin ransu kan wannan sabon mataki Wannan ya biyo bayan barazanar da ASUU take yi na sake komawa yajin aiki.
Lapai, Niger – Hankalin dalibai ya tashi a jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai IBBUL, sakamakon karin kudin makarantar da hukumomin jami’ar suka yi.
A ranar Talata, shugabannin jami’ar sun sanar da dalibai cewa an kara kudin makarantar ga dukkan dalibai.
Read Also:
A cewar takardar sanarwar da Legit Hausa ta samu ranar Alhamis wacce Rijistran jami’ar, M.A Abdullahi ya rattafa hannu, dalibai zasu fara biyan kudi har N200,000
A karin da aka yi, sabbin dalibai yan asalin jahar Neja zasu fara biyan N129,675.00 yayinda tsaffin dalibai zasu fara biyan N67,925.00. Dalibai kuma wadanda ba yan asalin jahar ba zasu fara biyan N200,210.00 yayinda tsaffin zasu fara biyan N117,325.00.
Wani sashen sanarwan yace:
“Muna sanar ga daukacin jama’a, musamman iyaye, sabbi da tsaffin daliban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai, cewa shugabannin makarantar a zamansu na 50 ranar Talata, 1 ga Yuni, 2021, sun amince da kara kudin dukkan dalibai daga sabuwar kakar 2020/2021.”
“Saboda haka, dukkan sabbi da tsaffin dalibai su fara rijista ranar 16 ga Agusta, 2021. Duk wanda kuma bai yi da wuri ba za’a ci shi tara.”