Zahra Bayero: Malamin Addinin Islama ya yi Tsokaci kan Shigar Amaryar Yusuf Buhari

 

Malamin addinin Islama ya yi tsokaci kan yadda amare ke sanya kayan da suka saba addini lokutan bukukuwansau.

Malamin ya kuma ja wo hankalin Zahra Bayero a gefe guda kan wani shiga da ta yi a bikin wankar amarya na aurenta.

Malamin ya yi nuni da irin hatsarin dake tattare da irin wannan shiga, yana mai cewa, ya kamata a duba lamarin.

Kano – Babban Malamin addinin Islama, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi tsokaci game da shigar da Zahra Bayero; amaryar Yusuf Buhari, yana mai nuna takaicin yadda ‘ya’yan musulmai suka baci da shigar nuna tsiraici.

A makon nan wasu hotuna suka watsu a kafafen sada zumunta, wadanda ke nuna Zahra Bayero, budurwar da dan shugaban kasa Buhari zai aura sanye da wasu kaya masu nuna wane bangare na jikinta.

Wannan shiga da tayi ya jawo cece-kuce, yayin da mutane da dama suka nuna damuwarsu da cewa, wannan shiga bata yi dace da addinin Islama ba, kamar yadda budurwar take musulma.

Malamai a bangare guda, sun yi tsokaci kan lamarin, inda shahararren malami Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi tsokaci mai tsoratarwa kan wannan shiga.

Nasihar malamin bata tsaya kan Zahra kadai ba, malamin ya yi kira ne ga dukkan masu irin wannan shiga, yana mai tuna yadda ake samun ‘ya’yan manya a kasar nan da irin wannan dabi’a.

A jiya Laraba 4 ga watan Agusta, malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook inda Legit Hausa ta gano yana cewa:

“1. Lalle irin yadda amare ‘ya’yan musulmi suke yin shiga ta nuna tsiraici a mahangar Musulunci sannan kuma su dauki hotunansu cikin wannan shiga ta fitsara su watsa wa Duniya, abin takaici ne matuka. Kuma abu ne da zai iya jawo hushin Allah a kan al’ummar Kasa. ”

2. Lalle mun ga irin wannan fitsara, da saba Shari’ah, a ‘yan shekaru kadan da suka wuce daga wata ‘yar shugaban kasa, muka kuma sake ganin irinta daga wata ‘yar gwamna, ga shi a yau kuma muna ganin ta daga wata ‘yar babban sarki!!

“3. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki cewa kada Ya kama mu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa. Ameen.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here