Ina Neman Afuwar Al’ummar ƙasa Game da Wahalhalun da Wasu Tsare-Tsarenmu Suka Haifar – Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari ya nemi afuwar al’ummar ƙasar game da wasu manufofin gwamnatinsa waɗanda ya ce ya san sun haifar da damuwa tsakanin al’umma.
Shugaban ya faɗi hakan ne a jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasar, karo na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa.
A lokacin da yake bayani kan tattalin arziƙi, shugaba Buhari ya ce “Tattalin ariziƙinmu (Najeriya) ya ƙara zamantowa mai jurewa saboda irin matakan da aka ɗauka domin ganin cewa bai durƙushe ba a lokacin da tattalin arziƙin duniya ya shiga mummunan hali.”
Ya ƙara da cewa “A ƙoƙarin inganta tattalin arziƙin mun ɗauki matakai masu matuƙar wahala waɗanda yawancinsu suka samar da sakamako mai kyau.”
“Wasu daga cikin matakan sun haifar da wahalhalu, kuma ina mai neman afuwar al’ummar ƙasa game da hakan. Sai dai mun ɗauki matakan ne domin amfanin wannan ƙasa.”
A ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 ne gwamnatin shugaba Buhari ke zuwa ƙarshe bayan kwashe shekara takwas yana mulki.
Kuma a ranar ce sabuwar gwannati za ta kama aiki inda za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, bayan lashe zaɓen da ya yi a watan Fabarairu.
Read Also:
Jawabin Shugaba Buharin na ƙarshe ya tabo lamurra da dama, ciki har da ƙoƙarinsa na yaƙi da rashawa.
Shugaba Buhari ya ce “Ƴan uwana ƴan Najeriya kun san yadda, har cikin zuciyata nake matukar so na ga na yaƙi rashawa wanda shi ne ya hana ƙasar ci gaba. Na yi bakin ƙoƙarina wajen ganin an ci nasara duk da irin turjiyar da muka samu wadda da ma mun yi tsammanin hakan.”
“Ina murna kan cewa an samu nasarar ƙwato kuɗaɗe an dawo da su gida kuma an ƙwato kadarorin da aka saya da kuɗin haram”
A batun tsaro shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta, inda ta samu nasarar “rage kaifin ayyukan ƴan bindiga da ta’addanci da fashi da makami da sauran ayyukan ɓarna.”
Buhari ya kuma buƙaci al’ummar Najeriya su kasance masu taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar lura da abubuwa da ke faruwa a yankunansu domin ganin an ɗora kan nasarar da gwamnatinsa ta samu.
Ya kuma ce “Har yanzu ina takaicin yadda ake ci gaba da garkuwa da yaranmu. Ina jajanta wa iyaye da abokai da ƴan uwan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan harƙalla da tashin hankali. Dakarun tsaronmu na aiki babu dare ba rana domin ganin sun karɓo waɗanda har yanzu ake garkuwa da su.”
Muhammadu Buhari ya ƙara da cewa ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya sauke nauyin da ya ɗauka na mulkin ƙasar, kuma zai ci gaba da yi wa ƙasar addu’a bayan sauka daga mulki.