Jam’iyyar NNPP ta yi Karin Bayyani Kan Raɗe-Raɗin Komawar Kwankwaso APC

 

Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da raɗe-raɗin da ake yi na cewa ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC.

Sakataren jam’iyyar ta NNPP na ƙasa, Dakta Major Agbo ne ya bayyana hakan, ranar Asabar a wani taro na manema labarai a Abuja.

Ya ce babu wani aibu dangane da ganawar da Kwankwaso ya yi da Tinubu a birnin Paris na Kasar Faransa, saboda a cewarsa, Kwankwaso mutum ne na mutane.

Abuja – A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne jam’iyyar NNPP ta kwantarwa da magoya bayanta hankali kan tunanin da suke na komawar ɗan takararta Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Jam’iyyar ta NNPP na mayar da martani ne dangane da ganawar da aka yi tsakanin Kwankwaso da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a Paris da ke ƙasar Faransa, jaridar The Punch ta yi rahoto.

Ganawar ta Kwankwaso da Tinubu a Faransa ta janyo muhawara mai zafi a tsakanin al’umma, inda anan wasu suka fara raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai koma APC.

Kwankwaso mutum ne na mutane Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dakta Major Agbo, a wani taron manema labarai a Abuja, ya tabbatarwa da ‘yan jam’iyyar cewa babu wani aibu a cikin haɗuwar ta Kwankwaso da Tinubu.

Ya bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasar da yake da mutane a ko ina ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ba.

A cewar sa:

“Ba na so ku ji tsoron cewa zai tafi wani wuri. Babu inda zai je. Kamar yadda na faɗa, shi mutum ne mai mutane a kowace jam’iyya ta siyasa. Za ku ga irin hakan da dama a gaba.”

Ya kuma ce nasarar zaɓen gwamnan jihar Kano da Abba Kabir, da mataimakinsa Aminu Gwarzo suka samu za ta haifar da sabon yanayi.

A halin da ake ciki, hadiman Tinubu da na Kwankwaso sun bayyana kwarin guiwar ƙawancen da aka samu tsakanin shugabanninsu.

Sun bayyana cewa hakan na nuni da yadda ya kamata a ce gwamnatin haɗaka ta kasance. Wannan dai na zuwa ne tun bayan haɗuwar zaɓaɓɓen shuganaban ƙasar da Kwankwaso a birnin Paris da ke Faransa.

Batun ci-gaban ƙasa Tinubu ya tattauna da Kwankwaso

Ɗaya daga cikin tsofaffin ‘yan gidan siyasar Tinubu, kuma tsohon darakta-janar na yaƙin neman zaɓensa, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce babu batun komawar Kwankwaso APC.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here