2023: Saraki ya yi Kira ga Masu Neman Kujerar Shugaban Kasa

 

Bukola Saraki ya ce duk wanda ya karkatar da hankalinsa wurin neman kujerar 2023 a yanzu, baya da kishin Najeriya.

A cewar tsohon shugaban majalisar dattawa, kasar nan tana cikin mawuyacin hali, kamata yayi a nemi maslaha.

Ya kara da cewa, ya kamata ‘yan jam’iyyar PDP su dakata da yakin neman zabe, a fara magance matsalolin tsaron Najeriya.

Bukola Saraki, shugaban kwamitin sasanci na jam’iyyar PDP ya ce yakamata shugabanni su dakata da neman kujeru, su hada kan ‘yan kasa, a gyara makarantu sannan su janye duk wasu matsalolin da ke raba kawunan al’umma.

Ya shawarci shugabanni masu neman kujerun siyasa, da su dakata na wucin gadi, a gyara kasar nan tukunna. Yakamata su nuna cewa su ‘yan kasa nagari ne, Premium Times ta wallafa.

Saraki ya ce, “Duk wata jam’iyya ko kuma dan siyasa wanda bai damu da matsalar da ke addabar kasar nan ba a wannan lokacin, bai cancanci rike wani mukami ba a kasar nan.

“A yanzu, babu abinda yafi Najeriya muhimmanci.”

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce, alamu sun nuna ba nasarar PDP kadai Najeriya take bukata ba don ta farfado ta koma yadda take.

Ya yi wa shugabannin jam’iyyar PDP alkawarin cewa kwamitin sasancin jam’iyyar za su yi iyakar kokarin yin ayyukansu yadda ya dace.

A cewar Saraki, tuni kwamitin ta fara ayyuka a kan yadda za ta nemi hadin kan ‘yan jam’iyyar.

“Mun riga mun tattauna kuma mun zauna da gwamnoninmu, wadanda su ne za su jagorancin hadin kan al’umma.

“Ina alfaharin sanar da kowa cewa har yanzu PDP ce kadai jam’iyyar da za ta iya hada kan ‘yan Najeriya kuma tayi gyara yadda ya kamata.

“Alamar muhimmancin jam’iyyar shine, ita ce kadai jam’iyyar da take da a kalla ko gwamna daya ne a kaf yankunan da ke kasarn an.

“Sannan jam’iyyar ce kadai take da mai mukami a kowanne yanki, mazaba, kananun hukumomi, jihohi da ko ina a fadin kasar nan,” yace.

An sha cewa “Duk wani layi ko anguwa, wanda ba a ga alamar lema ba, ba cikin Najeriya take ba.”

A cewar Saraki, duk da akwai alamar a 2023 PDP za ta yi nasara, amma akwai bukatar ‘yan jam’iyyar su hada kawunansu don cimma nasara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here