Newcastle ta Doke Arsenal a Gasar Caraboa
Fatan Arsenal na lashe kofin farko a kakar bana ya gamu da cikas bayan da Newcastle ta yi waje da ita a gasar Carabao da suka fafata a filin wasa na St. James’ Park.
Rashin nasarar da Arsenal ta yi a gidan Newcastle na nufin ta sha kaye da ci 4-0 gida da waje da suka buga a matakin wasan kusa da na ƙarshe na gasar.
Read Also:
Ƙungiyar – da Mikel Arteta ke jagoranta – yanzu za ta mayar da hankali kan kofin Premier da take fatan lashewa, bayan da take mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Liverpool ta ɗaya.
Haka kuma Gunners ɗin ta kai matakin wasan zagayen ‘yan 16 a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Rabon da Arsenal ta ɗauki wani kofi dai tun 2020 lokacin da ta ɗauki kofin FA Cup