Ambaliyar Ruwa: An Saka Dokar Ta-ɓaci a Birnin New York da Jahar New Jersey
An sanya dokar ta-ɓaci a birnin New York da kuma jahar New Jersey mai makwabtaka yayin da ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya haifar ya mamaye wasu sassan arewa maso gabashin Amurka.
Read Also:
Hukumar hasashen yanayi ta Amurkar ta ce ruwan saman da ake ci gaba da zabgawa na barazana ga rayuwaka.
Wasu hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya shanye motoci a bisa titunan da suka zama koguna inda kuma ruwan yake ci gaba da kwarara cikin tashoshin jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.
Rahotanni sun ce aƙalla mutum 10,000 ne ke zaune dunɗum ba tare da wutar lantarki ba.