Ya Musanta Jita-Jitar da Ake Akan IPPIS na ASUU –  Ngige

Ministan Kwadago ya yi fashin baki kan tattaunawa gwamnati da ASUU ranar Juma’a.

Ya musanta maganar cewa a cire malaman jami’o’i daga manhajar IPPIS.

Gwamnatin tarayya ta yiwa ASUU tayi N65bn na alawus da gyaran jami’o’i.

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an togaciye mambobin kungiyar malaman jami’a ASUU daga manhajar biyan albashin IPPIS har abada.

Ministan Kwadago da aiki, Chris Ngige, ya bayyana cewa an yiwa gwamnati mumunan fahimta ne saboda ba tayi yarjejeniya da ASUU cewa za ta ciresu daga manhajar ba, Vanguard ta ruwaito.

Ministan ya bayyana cewa a zamansa da ASUU, gwamnati ta yi yarjejeniya da su cewa za’a biya malaman jami’ar da basu yi rijista a IPPIS ba albashinsu na Febrairu zuwa Yuni ta manhajar GIFMIS.

Ya kara da cewa za’ayi amfani da GIFMIS ne na wucin gadi.

A cewarsa, za a cigaba da biyan malaman kafin a kammala gwajin manhajar UTAS da suka gabatar domin tabbatar ingancinta.

“Ina ga abinda zai fi shine ka samu takardar tattaunawanmu, saboda mutane da yawa na fadin abubuwan da bamu fadi ba cewa mun yi watsi da IPPIS kuma wai ba zamu amfani da shi ba, wannan ba gaskiya bane, ” Ngige yace.

“Abinda muka tattauna a zaman shine yayinda hukumar NITDA da ofishin NSA ke gwajin manhajar UTAS, mambobin ASUU da basu rijista a IPPIS ba za’a biyasu ta tsohon manhajar (GIFMIS).”

Mun kawo muku cewa bayan watanni 8 ana muhawara, gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami’a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma’a, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami’o’i.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here