Ngozi Okonjo-Iweala: Duk da Haka, Ina sa Ran a ji Alheri a Zaben WTO
Okonjo-Iweala ta ji dadin goyon bayan da kasashen Duniya su ka ba ta.
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta nuna cewa ta na sa ran ta kawo kujerar WTO – Amurka ba ta goyon bayan Okonjo-Iweala mai takardar zama ‘yar kasa.
Ngozi Okonjo-Iweala wanda kafarta daya ta ke kan kujerar WTO ta ce duk da je-ka-ka-dawon da ake samu a zaben da ta shiga, tana hango nasara Jaridar. Punch ta ce Okonjo-Iweala wanda ta rike har darekta a babban bankin Duniya ta ji dadin yadda kasashen Duniya su ka ba ta goyon-baya.
Read Also:
“Ina farin cikin nasara da cigaban da na samu a takarar shugabancin @WTO. Kai na a kasa, da aka bayyana ni a matsayin wanda ta fi kuri’a tsakanin ‘ya ‘yan kungiya, kuma wanda ta fi yiwuwar samun mubaya’a.”
Okonjo-Iweala ta cigaba da cewa: “Za mu tafi zuwa mataki na gaba a ranar 9 ga watan Nuwamba.” Jawabin Ngozi Okonjo-Iweala shi ne na farko tun bayan da labari ya bayyana cewa ita ce ta ke kan gaba a kuri’ar da aka yi tsakanin kasashe 164 na kungiyar.
“Za mu cigaba da sa rai.” Inji mutumiyar Najeriya mai shekaru 66.
Kalubalen Okonjo-Iweala shi ne rashin goyon bayan Amurka, inda kasar ta ke tallata wanda ta rage a takarar wannan kujera, Yoo Myung-hee. A lokacin da Okonjo-Iweala ta rike kujerar Darekta a bankin Duniya, sun zo da wasu tsare-tsare da ba dole ba ne su kwanta wa shugaban Amurka Donald Trump. A baya gwamnatin Donald Trump ta nuna wa Akinwumi Adesina irin wannan adawa a AfDB.