NHRC ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 752 da ke da Nasaba da Cin Zarafi a Jihar Filato

 

Hukumar kare haƙƙin bil adama a Najeriya ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 752 da ke da nasaba da cin zarafi a jihar Filato tsakanin Janairu zuwa Nuwamban 2023.

Wata jami’a a hukumar, Veronica Abe ce ta bayyana haka ranar Litinin a birnin Jos.

A cewar Abe, ƙorafe-ƙorafen sun shafi na tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba da kisan kiyashi da cn zarafi da fyaɗe da auren dole da ƙin ba da gado.

Jaridar Punch ta ruwaito jami’ar na cewa an kammala bincike kan galibin ƙorafe-ƙorafen sai dai akwai waɗanda ake aiki a kansu.

Ta ƙara da cewa lamarin ya shafi mutum 1,053 har da mata 166 da yara 463.

Jami’ar a hukumar ta kare haƙƙin bil adama ta tabbatar da cewa nan ba da daewa ba za su kammala aiki kan ƙorafe-ƙorafen da suke ƙasa.

Ta kuma yi kira ga mazauna jihar ta Filato da su kai rahoton cin zarafi zuwa hukumomin da suka dace domin ɗaukan mataki.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com