Niger Delta Avengers: Shugaba Buhari ya Bukaci Kungiyar da su Dena yi wa Kasa Barazana
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci tsagerun Neja Delta su mayar da takubansu su dena yi wa kasa barazana.
Shugaban kasar ya ce babu bukatar sabbin barazana a yanzu duba da cewa ya amince ya biya musu kusan dukkan bukatunsu.
Shugaba Buhari, a ranar Juma’a 25 ga watan Yuni ya gana da shugabannin Neja Delta a fadarsa a Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana barazanar da kugiyar Niger Delta Avengers ta yi na fara kaiwa rijiyoyin man fetur da wasu kayyayakin hari a yankin kudu maso kudu a matsayin abin da ‘ba a bukatarsa’ a yanzu, The Cable ta ruwaito.
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, a shafinsa na Facebook ya ce shugaban kasar ya tattauna da shugabanin kungiyar yan Niger Delta da Ijaw, INC, a fadarsa a ranar Juma’a.
Read Also:
Sun ce yankin na kudu maso kudu shine mafi koma baya wurin cigaba a kasar kuma ba a yin wani yunkurin samar da bukatunsu.
A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Asabar, ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka mata.
Ta kuma nuna kin amincewarta da kungiyar Pan Niger Delta Forum, PANDEF, da Cif Edwin Clark ke yi wa jagoranci.
Buhari, ta bakin kakakinsa Femi Adesina, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce ya riga ya dauki mataki a kan mafi yawancin batutuwan da yan bindigan na Neja Delta suke kokawa a kai.
Sanarwar ta Buhari ta ce abin daure kai ne ganin sabbin barazana daga kungiyar kasa da awanni 48 bayan ganawarsa da shugabanin yankin Neja Delta inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin kamar sauya tsarin mulki da zaben kwamitin NDDC.
Buhari ya yi wa tawagar na yankin Neja Delta alkawairn cewa gwamnatinsa na aiki tukuru don ganin an biya musu bukatunsu da suka shafi matsalolin muhalli, cigaba da yankin da sauransu.
Ya kuma nemi hadin kai da goyon baya daga shugabannin yankin da mutane domin ganin ba a sake bannatar da kudade ba a hukumar kamar yadda aka yi a baya.