Gwamnatin ƙasar Nijar ta Dawo da Dokar Hana Hawa Babura a Sassan Jahar Tillabery
Dokar hana amfani da babura don zirga-zirga a wasu sassan jahar Tillabery na Nijar da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da ita bayan taron kwamitin tsaro na ci gaba da aiki.
Mazauna yankunan ne suka buƙaci hukumomi su mayar da dokar bayan ɗage ta a matakin wucin gadi makwannin baya.
Yankin dai na fama da taɓarɓarewar tsaro, kuma ana zargin masu iƙirarin jihadi da yin amfani da babura wajen kai hare-hare tare da tserewa cikin sauƙi.