Sojojin Jamhuriyar Nijar na rike da Jakadan mu – Shugaban Faransa
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce sojin Jamhuriyar Nijar su na rike da jakadansu a kasar.
Macron ya ce yanzu haka yana ofishin jakadancin Faransa da ke Nijar inda sojin ne su ke ba shi abinci.
Wannan na zuwa ne bayan sojin Jamhuriyar Nijar sun bukaci jakadan Faransa ya fice daga kasar dama sojojinsu
Paris, Faransa – Shugaba Emmanuel Macron ma Faransa ya bayyana cewa sojoji a Jamhuriyar Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa.
Read Also:
Macron ya ce sojin sun ajiye jakadan ne a ofishin jakadancin kasar, inda ya ke zargin sojojin da toshe hanyar kai kayan abinci ga ofishin.
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma’a 15 ga watan Satumba, TRT Afirka ta tattaro.
Ya ce yanzu haka jakadan kasar ya dogara ne a kan abin da sojojin suke ba shi tun da sun hana kai abinci zuwa ofishin.
Ya ce:
“A yanzu haka, akwai jakadanmu da kuma wani jami’in diflomasiyya da su ke tsare a ofishin jakadancin Faransa.
“Sun hana a kai kayan abinci wanda a yanzu abincin da suka ba shi yake ci.”