Hukumar NCC ta ce za’a Daina yi wa Marasa NIN Fasfo da Lasisin Tuki

 

Hukumar dake lura da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC ta shawarci masu amfani da harkokin sadarwa su hada layukan wayarsu da lambarsu ta katin dan kasa nan da ranar 31 ga watan Oktoba, wanda shi ne wa’adin da aka sanya.

Hukumar ta ce nan ba da jimawa ba za a fara hana wadanda ba su da lambar NIN damar samun wasu abubuwa na gwamnati ciki har da lasisin tuki da fasfo.

Da yake bayani cikin wani shiri na kai tsaye daraktan kula da harkokin jama’a Dr. Ikechukwu Adinde, ya shawarci mutane da su yi amfani da wannan dama ta kara lokacin rijistar da aka yi zuwa ranar 31 ga watan Oktoba domin hada NIN da layikan wayarsu.

“Kwanan nan za a fara hana mutanen da ba su da NIN damar samun wasu abubuwan da suke da bukata a rayuwarsu ciki har da lasisin tuki da na fasfo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here