Sai Wanda Yake da NIN za a Sayar wa da Shinkafa N40,000 – Gwamnatin Najeriya

 

Gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da sayar da shinkafa ƴar gwamnati kilogram 50 kan farashin N40,000.

Amma gwamnatin ta ce sai wanda yake da lambar katin ɗan ƙasa za a sayar wa shinkafar, kamar yadda ministan noma Abubakar Kyari ya bayyana.

Sai dai a sanarwar da ministan noman ya wallafa a shafinsa na Twitter, bai bayyana cibiyoyin da ƴan Najeriya za su samu shinkafar ba ƴan gwamnati

Tun a watannin baya gwamnati ta ce za ta karya farashin shinkafa domin rage wa ƴan ƙasar raɗaɗi, tsadarta a kasuwa.

Gwamnatin ta ce ta tanadi shinkafa ton 30,000 wanda aka gyara da za ta sayar a farashi mai rahusa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here