Yadda Shugaban NITDA ya Sanya Farin Ciki a Zukatan Marayu a Jahar Jigawa

 

Yara marayu na daga cikin rukunin mutane waɗanda bakasafai al’umma ke damuwa da duba da halin da su ke ciki ba, balle har su kai ga tunanin ware wasu maƙudan kuɗaɗe wajen tallafawa rayuwarsu ba, sai dai kuma mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) ya sha bamban da saura domin kuwa ya kasance jami’in gwamnatin tarayya na farko ɗan asalin Jihar Jigawa wanda ya tuna da marayu a duk kafatanin ƙananan hukumomin Jihar guda (27) ya tallafa musu.

Kimanin buhun shinkafa (2700) Malam Kashif Inuwa Abdullahi ya ba wa kwamitin marayu na ƙungiyar Izala aka rabawa marayun a ƙarƙashin gidauniyarsa ta aikin alkhairi gami da tunawa da mahaifinsa, (Malam Inuwa Foundation).

A cikin jimillar buhun shinkafar guda (2700), kowacce ƙaramar hukuma ta samu jimillar buhu (100) ga gidajen marayu ɗari, wanda kuma aka rabar a ranar 5 ga watan Afrelu, zuwa 12 ga watan na Afrelu, 2022. Kwamitin marayu na ƙungiyar ta Izala su ne su ka haɗa sunayen marayun a kowacce ƙaramar hukuma birni da kewaye su ka zaɓo waɗanda su ka fi buƙata aka kuma ba su wannan tallafi batare da wani bambanci ko sanayyar alfarma ba, (cancanta zalla aka bi wajen zaɓo waɗanda aka ba wa).

Bayyana irin wannan aikin alheri wanda babu manufar tozarta waɗanda su ka amfana, kana kuma babu manufar riya cikinsa, ya na taimakawa ne wajen zaburar da sauran al’umma musamman mawadata wajen cigaba da samar da tsare-tsaren tallafawa yara marayu da sauran mutane masu rauni, gami da fitar da shakku da munanan zarge-zargen: (“ba a taimakawa” a zukatan jama’a kan shugabanni) wanda kuma addini bai ƙyamaci bayyana duk wani nau’in alkhairi da kykkyawar manufa ba.

Mutanen da su ka amfana, da ma sauran al’umma daban-daban, sun bayyana farin ciki matuƙa da godiyarsu bisa wannan abin alheri. Misali: Amina Shu’aibu, yarinya ce marainiya ƴar asalin ƙaramar hukumar Buji, ga abin da ta ce jim kaɗan bayan an ba ta tata shinkafar “Ni marainiya ce, babana da iyata duk sun mutu, yayana ne ya ke riƙe da ni, ina godiya da samun wannan tallafi Allah Ya saka da alkhairi”. Inji ta.

Shi ma wani dattijo wanda ya amfana mai suna Ali na Ali ɗan asalin ƙaramar hukumar Kiyawa, ya bayyana godiya da farin cikinsa gami da addu’a kamar yadda ya ce: “mun gode, Allah Ya yalwata dukiyar Malam Kashif Inuwa, Allah Ya saka masa da alkhairansa, Allah Ya kai ladan kabarin magabata”. Inji shi ya yin da aka ba shi.

A ɗaya gefen kuma, su ma shugabannin kwamitin marayun na kowacce ƙaramar hukuma sun bayyana godiya da farin cikinsu kamar haka: “wannan tallafi abu ne mai muhimmanci musamman duba da yadda ake fama da tsadar rayuwa, duk waɗanda aka tallafawa ba shakka sun ji daɗi, mu na fatan Allah Ya saka masa da alkhairi Ya kuma sanya sauran masu hali su yi koyi da shi”. Inji Malam Auwal Shu’aibu Musa Yayarin Tukur, shugaban ƙungiyar Izala na ƙaramar hukumar ta Buji.

Haka zalika, “mu na roƙon Allah yadda Malam Kashif Inuwa Ya kula da marayu Allah Ya kula da shi, Allah Ya sa randa zai bar duniya Ya bar nasa marayun shi ma Allah Ya kula masa da su, mun yi farin ciki matuƙa Allah Ya ji ƙan Malam Inuwa”. Cewar Malam Ibrahim Chiroma Birnin Kudu, ɗaya daga cikin shugabannin kwamitin marayu na ƙaramar hukumar Gumel.

Shi ma a nasa tsokacin, Malam Umar Usaini Jahun, shugaban kwamitin marayu na ƙungiyar Izala na Jahun, ya bayyana cewa: “mu na godiya marar iyaka ga Malam Kashif Inuwa bisa wannan taimako da ya yi, wannan ba wai abu ne farau na taimako da ya ke yi ba domin ni shaida ne banda wannan akwai abubuwa da dama na taimako da ya yi, mu na godiya sosai Allah Ya sa masa a mizani, Allahi Ya taimake shi kamar yadda ya ke taimakon addinin Islam”.

Su ma iyayen ƙasa, hakimai waɗanda rabon tallafin shinkafar ya gudana a kan idonsu, sun bayyana nasu farin cikin da godiya gami da fatan alkhairi, misali: “Babban fatana Allah Ya saka masa da alkhairi, Allah sa Ya gama lafiya, Allah Ya kai ladan ga dukkan magabata da su ka rasu, Allah Ya tsare dukkan abin ƙi, Allah Ya ƙara arziƙi, Allah Ya sa mutane dayawa su yi koyi da shi”. Inji mai girma sarkin ban Ringim, Hakimin Ɓaɓura, Alhaji Nata’ala Mustapha.

Shi ma a nasa jawabin, mai girma Hakimin Miga, Alhaji Sani Yakubu, ya bayyana cewa: “Wannan kusan shi ne karon farko da wani mutum wanda ba ɗan yankinmu ba ya kawo mana wannan abin alkhairi domin marayu da masu ƙaramin ƙarfi, mun gode Allah Ya saka”.

Haka zalika, “Ya kamata sauran mawadata su yi koyi, duk wanda ya ke da hali ya kamata ace ya na da irin wannan gidauniya ta Malam Kashif Inuwa saboda anan Arewa ne za ka ga almajirai wanda da ace da irin wannan gidauniya to da duk haka ba ta kasance ba, da an samu sauƙin matsalolin, mu na fatan sauran mawadata za su yi koyi, mun gode Allah Ya saka da alkhairi”. Cewar mai girma Sarkin Dawakin Gumel, hakimin Maigatari, Alhaji Sani Alhassan wanda Malam Yakubu Aminu ya wakilta wajen rabon.

Kafatanin marayun da su ka samu tallafin za su yi amfani da shinkafar ne tare da sauran ƴan gidansu, wanda ɗumbin jama’a ne su ke kwana babu abin da za su ci, wanda hakan kuma ya sanya mutane da dama godiya da addu’a gami da jinjinar fatan alkhairi ga Malam Kashif Inuwa bisa wannan tallafi ga marayun a daidai gaɓar da wasu masu iyaye rayen ma buƙata su ke tare da zaburar da sauran masu hali da su yi koyi domin jinƙai da agaji ga rayuwar marayu.

Garba Tela Haɗejia

Laraba, 12 ga watan Ramadan, 1443.

Laraba, 13 ga watan Afrelu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here