NITDA ta ba wa F.U.D Gudumawar Na’ura Mai Ƙwakwalwa Guda 150

Hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), bisa kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin zamani, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), a wannan rana ta ba da gudunmawar na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computers) jimillar guda (150) ga jami’ar gwamnatin tarayya da ke birnin Dutsen Jihar Jigawa, “Federal University Dutse”, (F.U.D).

A rahoton da jami’ar ta fitar ta cikin shafinta na sadarwa na (Facebook), sun bayyana cewa: daga cikin jimillar kwamfiyutocin, guda (100) waɗanda ake ɗorawa ne akan tebur, (Desktop Computers), samfurin kamfanin (Lenovo), sai kuma guda (50) na tafi da gidanka, (Laptops), samfurin ƙirar babban kamfanin nan na (HP).

Da ya ke jawabi a lokacin da ya ke gabatar da gudunmawar ga hukumar jami’ar, mai girma shugaban na (NITDA), Malam Kashif Inuwa, wanda Hannah Peter ya wakilta, ya bayyana cewa dalilin ba da gudunmawar shi ne domin a bunƙasa koyo da koyarwa na zamani a jami’ar.

A nasa martanin a ya yin da ya ke karɓan gudunmawar, muƙaddashin shugaban jami’ar, (VC), Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad, wanda shugaban tsangayar fasaha da kimiyyar zamantakewa, Farfesa Lawan Shu’aibu, ya wakilta, ya godewa shugaban na (NITDA), bisa wannan gagarumar gudunmawa wacce ya ce za ta taimaka wajen bunƙasa sha’anin koyo da koyarwa ta hanyar fasahar sadarwar zamani, tare kuma da cika babban burin shugaban jami’ar na ɗora ta akan turbar fasahar zamani.

Ƙarawa da cewa: “Shugaban (NITDA) mutum ne mai salo daban-daban, sannan mutum ne sahun farko wanda ya himmatu ka’in da na’in wajen samar da nagartattun ayyukan fasahar zamani a jami’o’in Nageriya domin ganin sun dace da (ƙarni na 21). Jami’armu ta (FUD) ta yi haɗin gwiwa akan abubuwa da dama tare da (NITDA), musamman a fannin harkar noma a ƙarƙashin cibiyarmu ta nazari da bincike kan noma, jami’armu ta na godiya ta musamman ga shugaban na (NITDA) akan wannan al’amari. Cewar shugaban (FUD), Farfesa Muhammad.

Lahadi, 20 ga watan Fabarairu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here