Hukumar NITDA Ta Horar Da `Yan Jarida 50 Ilimin Gano Sahihancin Labarai A Jihar Jigawa

A kokarin da ta ke yi wajen ci gaba da bunkasa kwarewar `yan jaridu akan harkar aikin jarida a zamanance, hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta kasa (NITDA), karkashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, ta bai wa `yan jarida da matasa masu ilimi a sabbin kafafen sadarwa na zamani kimanin su 50 horo akan ilimin gano tushe, da sahihancin labarai a kafafen sadarwa na zamani.

Mahangar Arewa ta ruwaito cewar horon na tsawon yini biyu, wanda hukumar NITDA ta dauki nauyi, yayin da kamfanin sadarwa na “Image Marchant Promotions Limited” (IMPR) masu wallafa Mujallar (PRNigeria), da (Economic Confidential Magazine), sai kuma kamfanin (Penlight Centre for New Media Innovation) suka gabatar da bada horon.

An kuma gudanar da horon a dakin taro na cibiyar horar da ma’aikata ta Jihar Jigawa, inda aka koyawa masu tasiri na sabbin kafafen sadarwa na zamani, da `yan jaridu ilimi da dabarun gano tushen labari da sahihancinsa da kuma dabi’u da halaye na kwarai wajen amfani da kafafen sadarwa gami da salon tafikar da aikin jarida a zamani.

A jawabin da ta gabatar na bude taron bada horon, shugabar sashen hulda da al’umma ta hukumar (NITDA), Hajiya Hadiza Umar, ta bayyana cewa horon bunkasa kwarewa na daya daga cikin ayyuka da burukan hukumar.

Sauran wadanda su ka gabatar da jawabai sun hada da tsohon shugaban gidan Rediyon Jihar Jigawa, Alhaji Sabo Abdullahi Guri, inda ya hori `yan jaridu a Najeriya wajen dabbaka kwarewa da dabi’u na kwarai a fagen tafikar da ayyukan.

A nasa jawabin babban Editan kafar sadarwa ta (PRNigeria), Malam Yusha’u Shu’aib, ya hori masu amfani da sabbin kafafen sadarwa na zamani da `yan jaridu da su kasance masu kula da takatsantsan wajen ayyukansu domin gujewa labaran karya da keta alfarma.

Mista Samuel Adeyemi, sakataren yada labarai na ma’aikatar sadarwa ta kasa, (NIPR), reshen Jihar Legas, ya gargadi `yan jaridu da masu amfani da sabbin kafafen sadarwar na zamani da su zama masu kula da kiyayewa da mutanen da ka iya yin amfani da su wajen yada munanan manufofi da akidoji.

Shugaban sashen ayyuka na cibiyar (Penlight), Malam Ɗahiru M. Lawal, ya baje bayanai akan yadda ake amfani da fasahohi da manhajoji na zamani wajen gano asali da tushen labarai da hotuna masu motsi da marasa motsi domin a gujewa yada labaran karya hadi da fatan sanar da al’umma sahihan labarai na zahirin gaskiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here