NITDA ta Fara ba da Horon Noman Zamani ga Manoma 100 a Jihar Ogun
Read Also:
A bisa kan layin tsarin tattalin arziƙin zamani kan tsare-tsaren zamar da Nageriya cikakkiyar ƙasa mai amfani da fasahar zamani, a hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), bisa kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin zamani, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), ta ƙaddamar da shirinta na noman zamani, “National Adopted Village for Smart Agriculture” (NAVSA), a Ogun.
Kimanin matasan manoma guda (100) za a horar tare da raba musu jari da taki da injin bayi bayan kammala horon na tsawon kwanaki biyar wanda aka ƙaddamar a yau a jami’ar aikin gona ta gwamnatin tarayya da ke birnin Abekuta na Jihar ta Ogun, Federal University of Agriculture.
Litinin, 21 ga watan Fabarairu, 2022.