Hukumar NITDA ta Raba Kayan Aiki da Jari ga Matasa 140 Wadanda ta ba wa Horo Kan Gyaran Waya a Jihar Jigawa

Hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ta yaye matasa jimillar mutum (140) a Jihar Jigawa waɗanda ta ba wa horo kan sana’ar gyaran wayar salula a zamance gami da sauran harkokin fasaha, kana kuma ta raba musu jari haɗi da kayan aikin gudanar sana’ar domin dogaro da kai.

Horon na tsawon yini huɗu wanda aka gudanar da shi a ranar 31 ga watan Janairu, zuwa 4 ga watan Fabarairu, 2022 a cibiyoyi gudan biyu da aka ware a cikin garuruwan Dutse da Haɗejia, kowacce cibiya ta ɗauki jimilla mutane saba’in.

Kayan aikin sun haɗa da manyan wayoyi na hannu (Tablet), da sufanun sincewa da ɗaure waya, gami da kuɗin sufuri da sauransu. An kuma ilimantar da matasan salo da dabarun warware natsalolin wayar hannu a zamance.

Ko da a can baya, hukumar ta (NITDA) bisa kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), ta ƙaddamar da irin wannan shiri a wasu daga cikin Jihohin ƙasar nan kamar Jihar Yobe. Manufar shirin ita ce fatan ganin matasa sun samu abin yi tattalin arziƙin ƙasa ya bunƙasa.

Litinin, 14 ga watan Fabarairu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here