NITDA ta Ƙaddamar da Shirinta na Noman Zamani a Birnin Tarayya Abuja

Hukumar (NITDA) ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), bisa kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin zamani, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), yau ta ƙaddamar da shirinta na noman zamani a birnin Abuja.

Shirin na zaman na haɗin gwiwa a tsakanin hukumar da kuma karkarar fasahar zamani ta birnin tarayya, “Abuja Technology Village” (ATV) da kuma cibiyar ƙere-ƙere ta ƙasa da hukumar ta samar a Abuja, wato “National Centre for Artificial Intelligence and Robotics” (NCAIR).

Jimillar mutane hamsin, 50, waɗanda aka zaɓo daga ƴan hidimar ƙasa, su ne aka fara ba wa horon noman zamanin, “National Adopted for Village Smart Agriculture (NAVSA), yau a karon farko cikin ranakun horon kamar yadda aka wallafa a shafin (Facebook) na hukumar.

Jim kaɗan da rufe taron bitar a wannan rana, Mista Lukman Lamid, jami’in hukumar (NITDA) a sashen tattalin arziƙin zamani, ya jagoranci tawagar zuwa duba gonar (DEMO) wacce za a yi amfani da ita wajen tafikar da aikin noman.

Manufar wannan shiri na noman zamani ita ce amfani da fasahar zamani wajen bunƙasa aikin noma da kayan amfanin gona gami da fatan sauƙaƙa harkokin noma cikin nasara da cigaba.

HOTUNA: Rotimi Popoola.

Talata, 30 ga watan Maris, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here