Shugaban NITDA ya Kai Ziyarar Gani da Ido Asibitin Gumel Tare da Ziyarar Girmamawa ga Mai Martaba Sarki

Mai girma shugaban hukumar (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a ya yin da ya kai ziyara garin Gumel a jiya domin ganewa idonsa yadda aikin tiyatar ido, rabon maganin ciwon ido, da gilashin ƙara ƙarfin gani ya ke gudana a babbar Asibitin Garin na Gumel.

Aiki ne wanda gidauniyar ƙasar Qatar da haɗin gwiwar gidauniyarsa ta Malam Inuwa su ke gudanarwa kyauta ga al’ummar Jihar Jigawa.

A cikin jawabin da ya gabatar a ya yin hira da manema labarai a wurin, Malam Kashif Inuwa ya bayyana cewa aikin ya biyo bayan bincike ne da su ka gudanar su ka tabbatar da cewar Jihar Jigawa na sahun farko na Jihohin da ke fama da yawan masu lalurar ido, sannan kuma, duk mutum ɗaya zai kashe kuɗi kusan Naira dubu ɗari idan har zai je a yi masa aikin tiyatar idon, wannan dalili ya sanya gidauniyar tasa ta nemo wannan aiki daga gidauniyar ta ƙasar Qatar don a taimakawa al’umma kuma za a cigaba da yin wannan aiki a duk shiyoyin Jihar Jigawa duka.

Tunda farko gabanin duba aikin, shugaban hukumar ta (NITDA), ya fara da kai ziyarar girmamawa ga mai marba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani (CON), kana kuma ya samu rakiyar mai girma ɗan majalissar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin; Gumel da Maigatari da Gagarawa da Suletankarkar, Onarabul Nazifi Sani Fulawa, da kuma mai girma shugaban ƙaramar hukumar ta Gumel, Onarabul Ahmad Rufa’i Gumel, da sauransu.

Ɗumbin al’umma waɗanda su ka amfana da shirin sun yi masa godiya da addu’o’i na fatan alkhairi bisa wannan aiki da ya samar dominsu.

Talata, 14 ga watan Yuni, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here