Shugaban NITDA ya Buɗe Katafaren Ɗakin Gwaje-Gwajen Ƙirƙira na Ƙasa

Mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamami ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a yau ya buɗe wani katafaren ɗakin zamani na gwaje-gwajen ƙere-ƙeren kayayyakin fasahar sadarwar zamani, wanda su ka samar a cibiyar ƙasa ta nazari da ƙere-ƙeren na’urori masu ɗabi’u irin na bil’adama, “National Centre for Artificial Intelligence and Robotics (NCAIR), da ke Abuja.

Testing Room

Samar da ɗakin gwaje-gwajen ƙirƙirar, wani ƙoƙari ne na cika umarnin da mai girma shugaban ƙasa Malam Muhammadu Buhari (GCFR), ya ba wa mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), na sabunta Nageriya tayadda za ta jagoranci Duniya wajen harkar ƙere-ƙeren kayayyakin fasahar sadarwar zamani kan kasuwanci.

Katafaren ɗakin gwaje-gwajen ƙirƙirar, ɗaki ne na zamani irin wanda ake da shi a ƙasashen duniya da su ka cigaba kan harkar fasahar zamani. An kuma wadata shi da dukkan wasu nau’ikan na’urori waɗanda masu nazari da baiwar kirkira su ke buƙata wajen samar da wata ƙirƙira ta fasahar sadarwar zamani ko gwada wani tunani da su ka yi domin tabbata.

Daɗi da ƙari, an kuma yi wa ɗakin rijista da gidauniyar ɗakin gwajin ƙirƙira ta duniya wanda ƙungiya ce ta duniya da ke samarwa, gami da ba da gudunmawa wajen haɓakawa gami da bunƙasa sabis ɗin ire-iren ɗakin a duk duniya.

Haka zalika, daga wannan rana ɗakin zai cigaba da kasancewa a buɗe ga duk ƴan Nageriya masu baiwa da fasahar ƙirƙira domin su samar da ƙere-ƙeren da su ka yi tunani a zahiri tayadda za su amfana su amfani ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here