NLC ta ba Tinubu Shawara Kan Dakile Zanga-Zanga a Fadin Najeriya
Shugaban kungiyar NLC a Najeriya, Joe Ajaero ya bayyana damuwa kan halin kunci da ake ciki inda ya ce kowa a fusace ya ke
FCT, Abuja – Kungiyar Kwadago a Najeriya ta ba Shugaba Bola Tinubu shawarar yadda zai dakile shirin zanga-zanga a kasar.
Kungiyar ta ce hanya daya mafi dacewa wurin dakile zanga-zangar ita ce tattaunawa da fusatattun matasan.
NLC ta ba Tinubu shawara kan zanga-zanga
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a jiya Litinin 22 ga watan Yulin 2024, kamar yadda Tribune ta tattaro.
Read Also:
Ajaero ya ce zanga-zanga ‘yanci ce ta ‘yan kasa inda ya ce miliyoyin ‘yan Najeriya sun fusata kan halin kunci da ake ciki a fadin kasar.
Ya ce mafi yawan iyalai a Najeriya ba su iya samun cin abinci sau biyu a rana yayin da suke rayuwa cikin kunci da talauci, cewar Channels TV.
Zanga-zanga: NLC ta kawo mafita ga Tinubu
“Yayin da ake kara kusantar ranar zanga-zanga, kungiyar NLC ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci shugabannin masu zanga-zangar.”
“Ana cikin mawuyacin hali, kowa a fusace ya ke a Najeriya wanda lokaci ne da ya kamata gwamnati ta tattauna ba yakar ‘yan kasa ba.”
“Maganar gaskiya ita ce ba za ka mauje yaro ba kuma a lokaci guda ka ce za ka hana shi kuka, ya kamata a dauk matakin da ya ce a daidai wannan lokaci.”