NLC ta Soki IMF Bisa Nesanta Kanta da Cire Tallafin Man Fetur
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya ta caccaki Asusun Lamuni bisa maganar cewa ba ita ba ce ta shawarci gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur.
A wata sanarwa da NLC ta fitar a ranar Lahadi, wanda shugabanta Joe Ajaero ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta soki IMF bisa shawarwarin da take bayarwa a matsayin hanyoyin farfaɗio da tattalin arziki, waɗanda a cewarta su ne suka jawo wahala da tsayar komai cak a Najeriya da sauran ƙasashen da suke bin irin shawarwarin kamar yadda Channels ta ruwaito.
Read Also:
Tun da farko, a wani taron manema labarai na IMF da bankin duniya da aka yi a Washington DC, darakta yankin Afirka na IMF, Abebe Selassie, ya ce cire tallafin man fetur mataki ne da gwwamnatin Najeriya ta ɗauka a cikin gida.
“Wannan maganar ta IMF cewa a cikin gida ne aka ɗauki matakin cire tallafin mai, amma sai ba ta bayyana irin rawar da suka takawa wajen jula akalar dokokin ƙananan ƙasashe ba. Duk da ƙoƙarin da IMF ke yi nesanta kanta da cire tallafin, mu mun san ita ce kan gaba wajen kira da a cire tallafin man fetur domin inganta tattalin arzikin irin waɗannan ƙasashen.
“IMF na so ta nesanta kanta ne saboda matsalolin da suka biyo baya, amma ai ƴan Najeriya ba wawaye ba ne. Mun riga mun san yadda matakan da shawawarinsu suka jefa Najeriya da ma wasu Afirka cikin damuwa,” in ji ƙungiyar.