Kungiyar NCL ta yi Allah Wadai da Kama Shugabanta
FCT, Abuja – Kungiyar kwadago ta yi martani bayan jami’an DSS sun kama Joe Ajaero a yau Litinin.
Kungiyar NCL ta yi Allah wadai da lamarin kuma ta bukaci a gaggauta sake shugabanta, Joe Ajaero cikin gaggawa.
Legit ta tatttaro abin da kungiyar kwadago ta fada ne a cikin wani sako da NLC ta wallafa a shafinta na Facebook.
NCL: ‘Ana cin zarafin ma’aikata a Najeriya’
Kungiyar yan kwadago ta NLC ta bayyana cewa ana cigaba da cin zarafin ma’aikata a fadin Najeriya.
Read Also:
NCL ta fadi haka ne bayan an kama shugaban kwadago na kasa, Joe Ajaero a birnin tarayya Abuja.
NCL ta bukaci a daina cin zarafin ma’aikata
Kungiyar kwadago ta wallafa cewa dole ne a daina cin zarafin ma’ikata a Najeriya ta hanyar kama shugabannin ta.
Yan kwadago sun ce baraza da cin fuska da ake musu a Najeriya dole ne a tabbatar da cewa sun zo karshe.
Yanzu haka Joe Ajaero yana ina?
Kungiyar kwadago ta bayyana cewa yanzu haka ana rike da shugabanta, Joe Ajaero a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Haka zalika kungiyar ta ce an kama Joe Ajaero ne yayin da zai tafi taron yan kwadago a kasar Birtaniya.