NNPC na Alfaharin Gano Arzikin Man Fetur

Da yiwuwan Arewacin Najeriya ta wadatu da arzikin man fetur kamar kudu.

Bayan watanni ana bincike, an gano arzikin mai a tafkin jihar Benue.

Najeriya na haran ajiyar danyen mai akalla gangan milyan 40 domin sayarwa kasashen waje.

An gano arzikin man fetur mai dimbin yawa a jihar Benue, kuma masana ilimin ma’adinan Najeriya ke jagorantan hakan, shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari ya bayyana haka.

Kyari ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bude bikin baja kolin kungiyar masu nema arzikin man fetur na Najeriya (NAPE) a ranar Alhamis.

Ya jaddada cewa kamfanin NNPC ta zage dantse wajen fadada ma’ajiyar arzikin danyen man feturin Najeriya zuwa ganga milyan 40 ta hanyar binciken arzikin a sassan Najeriya gaba daya.

Mele Kyari, wanda ya samu wakilcin shugaban sashen hulda da jama’a na NNPC, Dr Kennie Obateru, ya ce suna daukan wannan mataki na neman arzikin mai ne domin cimma manufar gwamnatin tarayya na cimma gangar danyen mai milyan 4.

“Ina farin cikin yabawa ayyukan kwarai da kuke yi da jajircewarku masananmu wajen neman arzikin mai aka gani a jihar Benue. NNPC na alfahari da mambobin kungiyar NAPE dake jagorantan wannan kokari,” Malam Kyari ya bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here