NNPC ba Zata Cigaba da Daukar Nauyin Tallafin Man Fetur ba – Mele Kyari

 

NNPC ta bayyana cewa karin farashin litar man fetur ba zai fara aiki ba sai ta kammala tattaunawa da kungiyar kwadago.

Babban manajan hulda da jama’a na NNPC, Kennie Obateru, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Juma’a.

A jiya ne babban manajan matatar, Mele Kyari, ya bayyana cewa NNPC ba zata cigaba da daukar nauyin tallafin man fetur ba Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ta ce za a cigaba da siyar da man fetur a farashin da yake har sai ta kammala tattaunawa da kungiyar kwadago.

Kennie Obateru, babban manajan hulda da jama’a na NNPC, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a.

Wannan cigaban na zuwa bayan Mele Kyari, babban manajan kamfanin yace NNPC ba za ta iya jurewa cigaba da biyan tallafin man fetur ba.

A yayin jawabi a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja, Kyari yace NNPC ba za ta iya jure cigaba da daukar dawainiyar biyan tallafin man fetur ba, don haka za a fara siyar dashi a farashinsa na kasuwa.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, ya ce NNPC tana biyan N100-120 biliyan a kowanne wata domin barin farashin man fetur a yadda yake.

“Farashin zai iya zama tsakanin N211 da N234 na lita daya. Ma’anar shine masu siyan man fetur basu biyan farashin, wasu ke biyan musu,” yace.

“A yau da muke magana, abinda matatar ke ciki shine ba za ta iya cigaba da daukar wannan dawainiyar ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here