NNPC ya Bayyana Dalilin Tashin Farashin Man Fetur

 

Kamfanin mai na NNPC ya yi karin haske kan tashin farashin man fetur da aka fuskanta a yau.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana haka ne ga ‘yan jaridu a yau Talata a Abuja.

Ya ce tashin farashin ba shi da alaka da karancin man fetur, ya alakanta hakan da ‘yan kasuwa.

FCT, Abuja – Shugaban Kamfanin mai na NNPC, Mele Kyari ya bayyana dalilin tashin farashin mai a safiyar yau Talata 18 ga watan Yuli.

Kyari ya ce wannan tashin farashin ba shi da alaka da karancin man fetur a kasar kamar yadda ake yadawa.

Ya ce tashin farashin man fetur din na da alaka da sauyin farashi daga ‘yan kasuwa, Punch ta tattaro. NNPP

NNPP ya bayyana dalilin tashin farashin man fetur

Kyari ya bayyana haka ga ‘yan jaridu bayan wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Abuja, TheCable ta tattaro.

Ya ce karin farashin daga ‘yan kasuwa ne kuma ya na iya yin sama ko kasa.

Ya ce:

“Wannan farashi ya danganci ‘yan kasuwa ne, wannan shi ne ma’anar ‘yan kasuwa su rinka gudanar da farashin.

“Farashin zai na sauyawa, wata rana ya yi sama wata rana kuma ya yi kasa.”

Wannan na zuwa ne bayan farashin man fetur ya tashi daga N540 a kan lita zuwa N617 a safiyar yau Talata 18 ga watan Yuli, cewar THISDAY.

Ya karyata rade-radin da ake cewa wai hakan na da nasaba da karancin mai din a kasar.

Ya ce akwai tulin mai a kasar kuma wadatacce Ya tabbatar da cewa:

“Wannan sauyin farashin ba shi da alaka da yawan mai da ake batarwa, ba wannan ne matsalar ba.

“Idan ka je kasuwa ka sayi kaya, za ka siyar a kasuwa yadda farashin wurin ya kama, babu batun cewa karancin mai ne ya jawo, ba mu da wannar matsalar.

“Muna da wadataccen mai a kasa, mun samar da mai har ma tsawon kwanaki 32, wannan ba matsala ba ne.”

A bangarensa, shugaban hukumar NMDPRA, Faroul Ahmed ya alakanta tashin farashin mai din da tsadar danyen mai a duniya.

Ya kara da cewa yawan kashe-kashen kudade yayin shigo da man a bangaren dillalan man fetur shi ma na daga cikin dalilan.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here