Kamfanin NNPC ya Daina Kula da Farashin Man fetur – Garba Deen Muhammad

 

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya musanta cewa shi ne ya kara farashin man fetur, inda ta ce ba laifsa ba ne kawo sabon farashi.

Kamfanin NPPC ya ce bai da masaniyar wani karin farashin man fetur kuma hakan ya zo ne a karkashin hukumar kula da harkokin man fetur ta NMPRA.

‘Yan Najeriya dai sun firgita a ranar Talata lokacin da aka samu rahoton cewa NNPC ta kara farashin man fetur.

FCT, Abuja – Kamfanin man fetur na Najeriya, (NNPC) ya ce bai ba da izinin sabon jadawalin farashin man fetur ba da ke yawo a kasar.

A cewar kamfanin, farashin man fetur ya fito ne a karkashin kulawar hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya NMDPRA.

‘Yan Najeriya sun kadu da sabon farashin man fetur

Garba Deen Muhammad, kakakin kamfanin na NNPC, ya bayyana cewa kamfanin ya daina kula da farashin man fetur.

Ya kuma ce, NNPC ba ta da masaniya kan karin farashin, yana mai cewa hukumar NMDPRA ce ta amince da farashin man fetur ba NNPC ba.

Bangaren ‘yan kasa kuwa, kowa ya shiga rudani a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 yayin da dillalan man fetur suka kara farashin mai daga N165 zuwa N179 kan kowace lita.

A binciken Legit.ng ta tattaro ya nuna cewa galibin ’yan kasuwa masu zaman kansu suna sayar da man fetur tsakanin Naira 170 zuwa 200 kan kowace lita wanda hakan ya saba wa umarnin gwamnatin tarayya.

NNPC ya kara farashin mai a gidajen mansa

A cewar Vanguard, ‘yan kasuwa da dama na ci gaba da siyar da mai akan farashin da suka ga dama a yankuna daban-daban.

Gidajen mai na kamfanin mai na kasa NNPC na sayar da man fetur a kan N169 a kan kowace lita a Legas yayin da manyan ‘yan kasuwa ke sayar da kan sama da N170 kan kowace lita.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here