Watanni Babu Wuta: NNPC Zai Samar da Wutar Lantarki a Jahar Borno

 

NNPC da wasu kamfanoni za su samar da wutar lantarki na gaggawa a Maiduguri.

Mutanen garin Maiduguri da kewaye sun dade suna fama da matsalar rashin wuta.

CMEC da GE za su bada gudumuwa a kafa tashar lantarki ta musamman a Borno.

Kamfanin man fetur na kasa, NNPC, da wasu kamfanoni sun sa hannu domin samar da wutar lantarki na gaggawa a fadin garin Maiduguri, jahar Borno.

NNPC da kamfanin CMEC na China Machinery Engineering da General Electric (GE), sun kulla yarjejeniyar EPC domin kawo aikin kayan gyaran wutan.

The Cable ta ce kamfanonin za su samar da megawatt 50 na karfin wutar lantarki cikin gaggawa.

A wata sanarwa da NNPC ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, ta tabbatar da cewa an kulla yarjejeniyar wannan kwangila.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, NNPC ta ce aikin gyaran wutan na Maiduguri zai inganta kokarin da ake yi na cin moriyar karfin gas a fadin Najeriya.

“Aikin zai taimaka wajen yaye kalubalen rashin wutar lantarki da ake fama da shi a babban birnin jahar Borno.”

A watan Afrilun 2021, shugaban NNPC na kasa, Mele Kolo Kyari, ya yi alkawarin za su yi maganin matsalar da mutanen Maiduguri da kewaye suke fuskanta.

“Muna tunanin zai yiwu a samar da tashar wutar lantarki a Maiduguri wanda zai magance matsalolin da ake fama da su, kuma ya kai wuta zuwa garuruwan kewaye, har zuwa wasu kasashe.”

Cikin kankanin lokaci, nan da watanni uku zuwa hudu ake sa ran za a kammala wannan aikin.

Idan aka cin ma nasarar wannan aiki, al’umma za su samu wutar lantarki nan da karshen shekara. Matsalar ta jawo abubuwa sun kara tsada a Maiduguri.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here