NNPC Sunyi Nasarar Samo Danyen Man Fetur a Arewacin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta na yunkurin nemo mai a yankin Arewacin Najeriya.

Ministan man fetur, Timipre Sylva ya bayyana irin nasarorin da ake samu.

Timipre Sylva ya ce an gano wasu rijiyoyi a Gombe a aikin da NNPC yake yi.

Karamin ministan harkokin mai na kasa, Timipre Sylva, ya ce an yi nasara a yunkurin neman danyen mai da NNPC ya ke yi a Arewa maso gabas.

Jaridar Punch ta ce Mista Timipre Sylva ya bayyana wannan a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba.

Ministan tarayyan ya ke cewa an hako rijiyoyi biyu na danyen mai a jihar Gombe, yayin da NNPC ke cigaba da laluben danyen mai yankin tafkin Chadi.

Da aka nemi Timipre Sylva ya yi bayani a game da inda aka kwana a aikin neman mai, sai ya ce: “Shakka babu mun tsunduma sosai a wannan aikin.”

“Mun riga mun samo mai. Mun hako rijiyoyi biyu yanzu a Arewa maso gabas, a yankin Gombe, an yi nasara, kuma za a cigaba da aiki a yankin Chadi.”

Sylva ya bayyana cewa gwamnatinsu ta karkashin NNPC za ta cigaba da wannan gagarumin aiki.

A na ta bangaren, gwamnatin jihar Gombe za ta bada goyon bayan domin ganin NNPC ya cigaba da laluben danyen mai har zuwa yankin kasar Gongola.

Gwamnatin tarayya ta ce duka al’ummomin jihohin da ake wannan aiki, a shirye suke da su bada gudumuwarsu wajen ganin NNPC ya hako danyen mai.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen ganin an samu mai a wajen Neja-Delta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here