Gwamnatin Norway ta Kori Jakadun Rasha 15 daga ƙasar
Gwamnatin ƙasar Norway ta kori jakadun Rasha 15 bayan zargin su da leƙen asiri, kafin sallamarsu daga Norway.
Jami’an na aiki ne a ofishin jakadancin Rasha da ke Oslo babban birnin ƙasar ta Norway.
Wannan dai wani sabon mataki ne a yaƙin da Norway ta ke yi da Jami’an leken asirin Rasha.
Read Also:
Ko a watan Oktobar bara, an kama wani mai bincike a jami’a a arewacin Tromso, wanda ya gabatar da kansa a matsayin Malamin Jami’a daga Brazil.
Bayan bincike an gano sunansa Mikhail Mikushin kuma ma’aikaci ne a hukumar leken asirin Rasha.
Ministan harkokin wajen ƙasar ya ce tun da farko an gano yadda jakadun Rashan da aka kora su ke wa su ayyuka da suka fi ƙarfin matsayinsu.