NSCDC Sunyi Nasarar Ceto Wata Mata Daga Hannun ‘Yan Uwanta
An yi nasarar ceto wata mata wacce ’yan uwanta suka kulle a wani daki tsawon wata biyar.
Matar da aka ceto mai suna Saratu Ayuba tana zaune ne a unguwar Bolari da ke garin Gombe.
An rufe matar ne bisa zarginta da ake yi da yin cikin shege tare da haifewa.
A karshen mako ne rundunaar tsaro ta NSCDC a jihar Gombe ta ceto wata mata yar shekara 35 wacce ake zargin yan uwanta sun kulle ta tsawon fiye da wata biyar.
An ceto Saratu Ayuba da ke zama a kwatas din Bolari a birnin Gombe sakamakon wasu bayanai da aka samu daga makwabta, bayan sun gano halin da take ciki na azabtuwa.
Wasu yayyenta maza ne suka rufe ta a daki tsawon sama da watanni biyar, bayan zargin cewa ta yi cikin shege da kuma haifewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
Shaidu sun bayyana cewa an daure Saratu da mari tare da jaririyar da ta haifa yar watanni biyu a cikin wani daki mara tsafta, a gidansu da ke Bolari.
Saratu, wacce ta tsinci kanta a cikin wani yanayi mara kyan gani ba tare da suturar kirki ba, ta ce shayi da biredi kawai ake bata sau daya a rana tsawon watanni biyar da tayi a kulle.
Saboda yanayin da take ciki na rashin samun kula, ta ce bata samar da wadataccen ruwan nono domin shayar da jaririyarta.
Ta bayyana cewa tsohon mijinta ne yayi mata ciki, inda ta kara da cewa da gangan yayi hakan domin tursasa yayyenta mayar da ita gidansa. Ta ce tsohon mijin nata yayi mata saki biyu bisa kuskure.
Ta kara da cewa tana da ’ya’ya biyu a aurenta na farko; Alkasim mai shekaru 10 da kuma Fatima shekara takwas.
Sai dai kuma, yayan Saratu mai suna Muhammad Tajuddin ya ce sun kulle ta ne bayan likitoci sun gano tana da tabin hankali.