NWC Sun Shiga Ganawa da Gwamnonin APC a Abuja
Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) sun shiga ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) a birnin tarayya Abuja.
Rahoto ya nuna cewa taron zai maida hankali kan shirye-shiryen manyan taruka biyu da ke tafe a mako mai zuwa.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, mataimakansa na kudu da arewa da sauran jiga-jigai sun halarci zaman yau Talata.
FCT Abuja – Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ta ƙasa (NWC) na ganawa mai muhimmanci yanzu haka da shugabannin ƙungiyar gwamnonin APC (PGF) a Sakatariyar jam’iyya da ke Abuja.
Wasu majiyoyi daga cikin APC sun shaida cewa wannan zama zai tattauna batun taron masu ruwa da tsaki da majalisar ƙoli (NEC) mai zuwa, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Jam’iyyar APC ta shirya gudanar da taron shugabannin da suka hau karagar mulki a inuwarta ranar Litinin mai zuwa yayin da taron NEC zai biyo baya ranar Talata.
Read Also:
Taron, wanda ya kunshi mambobin NWC karkashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, shi ne na farko tun bayan zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar gwamnonin APC.
Idan baku manta ba gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya samu nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyya mai mulki (PGF). Mahalarta taron sun haɗa da shugaban jam’iyya na ƙasa, Sanata Adamu, Sakatare, Sanata Iyiola Omisore; mataimakin shugaban jam’iyya (arewa), Sanata Abubakar Kyari, da mataimakin shugaba (kudu), Emma Enukwu.
Sauran sun haɗa da mataimakin sakatare na ƙasa, Barista Festus Fanuter; mataimakin shugaban jam’iyya (arewa maso yamma), shugaban matasa, shugabar mata da sauransu.
Jerin gwamnonin APC da suka halarci taron
Gwamnonin da aka hanga a wurin taron sun haɗa da, Hope Uzodinma (Imo), Yahaya Bello (Kogi), Abdulrahman AbdulRasak (Kwara); da Babajide Sanwo-Olu (Lagos). Sauran su ne, Biodun Oyebanji (Ekiti); Rabaran Hyibcent Alia (Benuwai); Malam Dikko Raɗda (Katsina); Mai Mala Buni (Yobe) da kuma Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe).
Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe, ta wakilci Malam Uba Sani a taron, kamar yadda ta wallafa a shafin Facebook.