Olusegun Obasanjo ya Siffanta Ahmad Joda a Matsayin ‘Dan Najeriya na Gaske Wanda ya Tabbatar da Hadin Kai da Cigaban Najeriya
An jinjinawa Alhaji Ahmad Joda da wasu tsaffin sakatarorin din-din-din kan hadin kan Najeriya.
A cewar Obasanjo, sun yi wannan gwagwarmaya ne lokacin juyin mulki a 1966.
Tsohon shugaban kasan ya siffanta Joda matsayin jajirtaccen dan Najeriya.
Read Also:
Ota, Ogun – Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda tsohon sakataren gwamnati, Alhaji ahmad Joda, da sauran manyan sakatarorin din-din-din suka kare Najeriya daga barkewa bayan juyin mulkin 1966.
Obasanjo, yayin aika sakon ta’aziyyarsa ta bakin mai magana da yawunsa, Kehimde Akinyemi, ya siffanta Joda a matsayin dan Najeriya na gaske wanda ya tabbatar da hadin kai da cigaban Najeriya.
A cewar Obasanjo, “Na san bai cin Joda da wasu Sakatarorin din-din-din irinsa lokacin tashin tashina a 1966, da Najeriya ta yi kaca-laca. Saboda Araba ya lashi takobin raba kasar nan.”
“Amma Ahmad Joda da sauran manyan jami’an gwamnati irinsu Philip Asiodu, Liman Ciroma, Alison Ayida ne suka tabbatar Najeriya bata balle ba.”