Kotu na Tuhumar Jami’an Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara a Kan SDG da Satar N241m

 

Kotun Tarayya da ke Legas ta ce hukumar EFCC ta rike wasu Naira miliyan 241.

Lauyoyin EFCC suna zargin an yi gaba da wadannan kudin ne daga baitul-mali.

Ana tuhumar Jami’an ofishin Mai ba shugaban kasa shawara a kan SDG da sata.

Lagos – Wani babban kotun tarayya mai zama a garin Legas ya zartar da cewa a karbe wasu kudi da aka karkatar daga ofishin hadimin shugaban kasa.

Ana zargin an yi awon gaba da N241m Alkali mai shari’a Nicholas Oweibo ya bada umarni a rike Naira miliyan 241 da aka yi gaba da su daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan SDG.

Jaridar The Nation ta ce Alkalin ya kuma yanke hukunci cewa a karbe wasu shaguna da ke kan layin Ekukinam, a unguwar Utako, birnin tarayya Abuja.

Nicholas Oweibo ya dauki wannan mataki ne bayan lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya shigar da kara.

Yadda aka tafka ta’adi a ofishin SDG

Hukumar EFCC ta bakin Rotimi Oyedepo, ta fada wa kotu cewa an boye wadannan kudi ne kashi-kashi; N65m, N61m, N50, da N65 a wasu bankuna biyu.

EFCC tace bincikenta ya nuna mata cewa an saye wannan shaguna da ke Abuja ne da kudin da aka karkatar daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara.

Rahoton yace Abdulsalam Bawa ne babban akawu a ofishin hadimin shugaban Najeriyar.

Ana zargin Bawa ya hada-kai da wasu ma’aikata aka yi satan.

Lauyan da ya tsaya wa gwamnati ya zargi wasu kamfanoni; Kouchdim Unity Nigeria Ltd da Lankass Global Ventures da hannu wajen wannan badakala.

“Mun bankado akwai wani gida da aka saya da dukiyar jama’a da aka wawura, Abdulsalam Bawa ya ci amanar da aka damka masa.”

Alkali Oweibo ya daga karar mai lamba ta FHC/L/CS/90/2021 zuwa 6 ga watan Satumba, 2021, domin a ji hukuncin karshe da za a yanke a kan dukiyoyin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here