Kujerar Sakataren PDP na ƙasa: Kotu ta Bukaci UDEH-Okoye da ya Maye Gurbin Anyanwu

 

Kotu ta bayyana kujerar Samuel Anyanwu, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Imo, ta sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa a matsayin wacce ba kowa a kanta.

Kotun wacce ke zamanta a Enugu ta bayar da umarnin ne a ƙarar da Nwabueze Ugwu ya shigar na a yarda da wanda ya maye gurbin Anyanwu, Sunday Udeh-Okoye.

Kotun ta tilasta wa wadanda ake ƙara da su amince da wannan umarni har sai lokacin da ta yanke hukunci.

Enugu, jihar Enugu – Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Enugu ta bayyana kujerar ofishin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa a matsayin wacce ba kowa a kanta.

Kotun ta bayyana hakan ne a ƙarar da Nwabueze Ugwu ya shigar a gabanta, cewar rahotom TVC.

A wani umarni na wucin gadi, kotun ta tilasta wa wadanda ake ƙara a ƙarar da suka haɗa da shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, sakataren jam’iyyar na ƙasa da su amince da Sunday Udeh-Okoye, wanda kwamitin zartarwa na shiyyar Kudu maso Gabas, ya kawo ya maye gurbin Anyanwu.

Daga nan ne kotun ta yanke hukuncin cewa Sunday UDEH-Okoye ya maye gurbin Samuel Anyanwu har sai lokacin da ta yanke hukunci kan ƙarar, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Meyasa kotun ta ƙwace kujerar Anyanwu?

A cewar mai shari’a C.O Ajah, wanda ya shigar da ƙarar ya kawo ƙarar ne a ƙarƙashin sashe na 38 doka ta 1 da sashe na 39 doka ta 1 na dokokin babbar kotun jihar Enugu ta shekarar 2020.

Kotun ta lura cewa ta gamsu da takardu 23 waɗanda mai shigar da ƙarar ya kawo a gabanta.

Sai dai an ɗage ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba domin cigaba da saurarenta.

A kwanakin baya ne masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Gabas a jihar Enugu suka yanke shawarar maye gurbin Samuel Anyanwu, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Imo.

Masu ruwa da tsakin sun maye gurbin Anyanwu na sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa da Sunday UDEH-Okoye a matsayin sabon sakataren jam’iyyar na ƙasa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com