2023: Doyin Okupe ya Marawa Peter Obi Baya
Wani sabon ci gaba ya samu a jam’iyyar PDP a daidai lokacin da zaben Najeriya ke kara kusantowa nan da 2023.
Doyin Okupe daya daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ya janye daga takarar.
Jigon na PDP, bayan ya bayyana matakinsa na ficewa daga takarar, ya bayyana goyon bayansa ga wani dan takara, Peter Obi.
Abeokuta, jihar Ogun – Dr Doyin Okupe, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP ya fice daga takarar shugaban kasa a 2023.
Okupe dai na daya daga jerin yan takarar da a baya suka nuna sha’awarsu ta neman gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jam’iyyar adawa ta PDP.
Jiga-jigai daga jam’iyyun siyasar Najeriya na ci gaba da ayyana kudurin gaje kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Read Also:
Daily Trust ta ruwaito cewa jigon na PDP, ya sanar da matakinsa na ficewa daga takarar a kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), Iwe Iroyin da ke Abeokuta a jihar Ogun a ranar Laraba, 30 ga Maris.
2023: Okupe ya marawa Peter Obi baya
Okupe ya ce shi da magoya bayansa za su goyi bayan takarar shugaban kasa ta tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, kuma suna nan daram sai ya samu tikitin PDP a zaben badi.
Ya kuma nemi duk sauran ‘yan takarar shugaban kasa a Kudu; Cif Dele Momodu, Sanata Pius Anyim, da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, da su bayyana goyon bayansu ga takarar Obi.
Okupe ya caccaki shugabancin jam’iyyar PDP na kasa kan yadda har yanzu ta gaza wajen warware shiyyar da za ta fitar da dan takarar shugaban kasa na gaba.
A makon jiya ne ya bayyana hakan ga ilahirin jama’a, jim kadan bayan da Atiku ya bayyana tsayawa takara a 2023 karkashin PDP.