Kotu ta Dakatar da Gwamna Ganduje Daga Rushe Shugabancin KACCIMA

Wata kotun tarayya da ke Jihar Kano wacce alkali Jane Esienanwan Inyang ta yi hukunci, ta dakatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga rushe shugabancin KACCIMA.

An samu rahoto akan yadda gwamnan ya bayar da umarnin rushe shugabancin cibiyar sakamakon rikicin da ya ke ta ruruwa a cikinta.

Dama ya kamata wa’adin shugaban cibiyar, Alhaji Dalhatu Abubakar ya kare ne tun watan Oktoban 2021, daga nan rikici ya dinga barkewa.

Kano- Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano, wacce alkali Jane Esienanwan Inyang ta yi hukunci ta dakatar da gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje daga rushe shugabancin cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da noma ta Jihar Kano, KACCIMA,

Har ila yau, kotun ta kara da dakatar da gwamnan da sauran wadanda ake kara daga nada Alhaji Lawan Sule Garo da Ambasada Muntari Gashash a matsayin kwamitin rikon kwarya na cibiyar kasuwancin Jihar Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayar da umarnin rushe shugabancin cibiyar tun bayan yadda rikici ya dinga ruruwa a cikinta.

Wa’adin shugaban cibiyar, Alhaji Dalhatu Abubakar ya kare ne tun watan Oktoban 2021 tun bayan nan hayaniya ta dinga tashi, daga wannan sai wata.

Ba Ganduje kadai aka maka kotun ba

Wata kara wacce lauyan Usman H Darma da sauran masu shigar da kara guda biyu, suka shigar mai kwanan wata 14 ga watan Maris na 2022 da 21 ga watan Maris na 2022, kotun ta umarci bangarorin biyu da su dakata daga rushe shugabancin da kuma nada shugabannin rikon mwarya har sai an kammala sauraron karar.

Cikin masu karar akwai Usman H Darma mai kara na farko, Umar Isma’il Umar, mai kara na biyu da kuma cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da noma a matsayin mai kara na uku, rahoton Daily Trust.

Wadanda ake karar sun hada da Alhaji Lawan Sule Garo (na farko) Ambasada Muntari Gashash na biyu, Gwamna Jihar Kano, Antoni janar na Jihar Kano da kuma kwamishinan ‘yan sanda a matsayin na hudu da na biyar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here