Shugaba Buhari ya Nada Gwamna Okowa a Matsayin Memba a Kwamitin Kawo Sauyi na Fannin Kiwon Lafiya
Muhammadu Buhari ya nada gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin memba a kwamitin kawo sauyi na fannin kiwon lafiya.
Kwamitin da shugaban kasa ya kaddamar a ranar Litinin yana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugabanta.
Wasu fitattun likitocin kiwon lafiya kamar Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, suma membobin kwamitin ne.
An nada Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mamba a kwamitin kawo sauyi a fannin kiwon lafiya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagoranta.
Read Also:
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, jaridar The Cable ta rawaito.
A cewar wata sanarwa da daya daga cikin hadiman shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, an kafa kwamitin ne don ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a bangaren.
Sauran membobin kwamitin sun hada da Osagie Ehanire, Ministan Lafiya da kuma Shugabannin Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Kungiyar Magunguna ta Najeriya, kungiyar ma’aikatan jinya da kungiyar gwaje-gwaje ta Najeriya, Vanguard ta rawaito.
Gidauniyar Bill & Melinda Gates da Vesta Healthcare Partners za su yi aiki a matsayin masu sa ido a cikin kwamitin.